logo

HAUSA

Fasahar Zamani Na Taka Rawar Gani Ga Ci Gaban Masana’antu Sin

2024-08-05 16:37:40 CMG Hausa

Tarihi ya nuna cewa ana iya kaucewa takunkumi ko kuma takunkumin ya zama wata hanyar samar da damammaki ga kasa. Kamar dai yadda takunkumin da Washington ta kakkabawa kayayyakin kasar Sin a shekarar 2023, ya zama wata albarka ga kasar, wanda ya karawa kasar saurin samun bunkasa bisa manyan tsare-tsare.

Takunkumin da Amurka ta kakkabawa kasar Sin ya karkatar da hankalin kasar zuwa ga raya masana'antun gargajiya, da noma da masana'antu na kiwon lafiya bisa manyan fasahohin zamani da kirkirarriyar basira wato AI. Tare da goyon baya mai muhimmanci daga gwamnati da al'ummomin ’yan kasuwa, da masana kimiyya na kasar Sin da masu bincike wadanda suka hada kirkirarriyar basirar AI da 5G wajen gudanar da ayyukan masana’antu tare da sassan tattalin arziki masu alaka da kere-kere, da samar da kayayyaki da hidimomi masu karko. Fitattun kamfanoni irin su Alibaba, Tencent da Huawei da masana’antar motocin lantarki da na wutar lantarki bisa sabbin makamashi da sauransu, sun taka muhimmiyar rawa a wannan sauyi na fasaha.

Ana iya danganta bunkasuwar fasahohin kasar Sin musamman ga matakin da gwamnati ta dauka da hangen nesa kan dabarun tsara manufofi game da zuba jari a fannin fasaha. Samun nasarar bunkasa amfani da AI ba wai kawai ya kara daukaka matsayin kasar Sin a fagen masana’antun duniya ba, har ma ya karfafa tasirinta a masana'antar fasaha ta duniya.

Wannan tunanin ya haifar da yanayin da kamfanonin Sin ke iya gogayya kafada da kafada da wasu manyan kamfanonin fasahar zamani na duniya, da kuma taka muhimmiyar rawa ta hanyar hadin gwiwa da kirkire-kirkire wadanda suka kasance jigon masana'antar kere-kere ta kasar Sin, wanda kuma ke baiwa dukkan masu ruwa da tsaki a fannin kwarin gwiwar samun ci gaba da kuma karfin da suke da shi.

An kara fayyace ci gaban masana'antar kere-kere ta kasar Sin ta hanyar bunkasar tattalin arzikinta na dijital, yayin da a shekarar 2023, adadin darajar kayayyaki na manyan masana'antu a cikin tattalin arzikin dijital ya kai kashi 10 cikin 100 na GDPn kasar. Wannan nasarar ta cimma burin ci gaban tattalin arzikin dijital na “tsarin shekaru biyar-biyar” karo na 14 wato daga 2021 zuwa 2025, shekaru biyu ke nan gabanin jadawalin. Nasarorin da aka samu sun nuna saurin bunkasuwar fasahohin kasar Sin don inganta karfinta a masana'antar fasaha ta duniya. (Mohammed Yahaya)