Rana ta 9 ta Olympics na Paris ta shiga tarihi ga kungiyar ninkaya ta maza ta Sin
2024-08-05 14:18:44 CMG Hausa
Kasar Sin da Amurka sun yi kankan-kan a teburin lambar yabo ta zinari a gasar wasannin Olympics ta Paris zuwa jiya Lahadi. Kasar Sin ta yi nasara a gasanni da dama a rana ta 9 ta gasar, ciki har da gasar ninkaya mai nisan mita 100 ta karba-karba ta maza, lamarin da ya kawo karshen shekaru 40 da Amurka ta dauka tana lashe gasar.
Gasar ta yi zafi da sai da aka tantance hoto domin gano wanda ya yi nasara, inda ‘dan wasan ninkaya na kasar Sin Pan Zhanle, ya wuce abokin karawarsa baAmurke a rukunin karshe na gasar, inda ya lashewa kasar Sin lambar zinari.
Kasar Sin ta ci gaba da kare kambunta a teburin wasan kwallon tebur bayan Fan Zhendong ya lashe lambar zinaren gasar ajin maza ta mutum dai-dai.
A gasar kundumbala ta maza ma, Liu Yang na kasar Sin ya lashe lambar zinari. (Fa’iza Mustapha)