logo

HAUSA

Sin ta gaggauta raya tsarin yaki da bala’un ambaliyar ruwa da fari

2024-08-05 10:39:23 CMG Hausa

Ma’aikatar kula da harkokin ruwa ta kasar Sin ta bukaci a ci gaba da daukar nauyin yaki da bala’un ambaliya da fari a zahirance, da inganta kwarewar tsara manufofi da ba da umurni ga ayyukan yaki da bala’un, da kuma kyautata tsarin aikin yaki da su.

Ma’aikatar ta bayyana haka ne cikin wasu shawarwarin da ta fitar a kwanan nan, dangane da gaggauta gina tsarin gudanar da ayyukan yaki da bala’un ambaliyar ruwa da fari.

Shawarwarin sun kuma bayyana cewa, ya kamata a ci gaba da horas da kwararru, da kara amfani da fasahohin zamani, don bada kyawawan nasihohi ga masu yanke shawara a wannan fanni. Kaza lika, ya dace a fidda sakon gargadi yadda ya kamata, da gaggauta aiwatar da matakai a zahirance, da tabbatar da bada umurni da aiwatar da shi ba tare da cikas ba. (Murtala Zhang)