logo

HAUSA

Mali ta sanar da katse huldar diplomasiyya da Ukraine

2024-08-05 10:20:11 CMG Hausa

Gwamnatin rikon kwarya ta kasar Mali, ta sanar da katse huldar diplomasiyya dake tsakaninta da kasar Ukraine nan take.

Gwamnatin ta sanar da haka ne jiya Lahadi, inda ta ce ta lura da wani furuci da ya raina ikon mulkinta da kakakin hukumar leken asiri ta sojojin kasar Ukraine Andrii Yusov ya yi a baya bayan nan, wanda ke tabbatar da hannun Ukraine cikin wani harin wasu kungiyoyi ‘yan ta’adda, da ya rutsa da mutane tare da lalata dukiyoyi ga sojojin Mali, a yakin da suke a arewa maso gabashin kasar.

Sanarwar ta bayyana matakin hukumomin Ukraine a matsayin wanda ya take ‘yancin kan Mali, ya kuma zarce lamarin da kasa da kasa za su iya shiga tsakani, haka kuma takala ce a bayyane ga kasar. Don haka, gwamnatin rikon kwarya ta kasar Mali ta yanke shawarar katse huldar diplomasiyya nan take da kasar ta Ukraine. (Fa’iza Mustapha)