logo

HAUSA

Jirgin kasa na maglev mai saurin gudu ya kammala gwaji a arewacin kasar Sin

2024-08-05 21:27:56 CMG Hausa

Wani sabon tsarin sufuri na jirgin kasan maglev mai saurin gudu ya kammala gwaji a lardin Shanxi na arewacin kasar Sin a kwanan nan, wanda ya nuna wani ci gaban da aka samu na jirgin kasan maglev mai matukar saurin gudu wanda ke iya tafiya kilomita 1,000 cikin sa’a guda.

An fara gina tsarin sufuri na jirgin kasan maglev mai saurin gudu a gundumar Yanggao a watan Afrilu shekarar 2022, wanda ya hada fasahar jirgin sama tare da fasahar sufurin jirgin kasa, da nufin samar da jirgin kasa mai saurin kilomita 1,000 a cikin sa'a guda.

A nan gaba, za a iya amfani da tsarin tsakanin manyan biranen kasar Sin, wanda zai ba da damar yin zirga-zirga daga Beijing zuwa Shanghai cikin kusan sa'a daya da rabi. (Yahaya)