logo

HAUSA

Yaduwar fasahar Juncao ta nuna sahihancin Sin

2024-08-05 14:22:16 CMG Hausa

Sinawa su kan ce, ba mutum kifi, bai kai koya masa dabarar su ba. Wannan ra’ayi na taimakon mutane ya nuna sosai, a kokarin kasar Sin na yayata fasahar Juncao a nahiyar Afirka.

A wajen wani bikin baje kolin fasahohin aikin gona da ya gudana a Kigali na kasar Rwanda a kwanan baya, wani mai masana’antu a kasar mai suna Emmanuel Ahimana ya ce, yadda ya samu damar koyon fasahar Juncao na kasar Sin ya sa shi farin ciki matuka. Ban da haka, duk a kwanan baya, Adhere Cavince, wani masharhanta na kasar Kenya, ya rubuta wani bayani da aka wallafa a jaridar Daily Nation ta kasar, wanda ya ce fasahar Juncao za ta taka rawar gani a kokarin kasar Kenya na kawar da talauci.

Juncao wani nau’in ciyawa ce da ake iya yin amfani da ita wajen noman laimar kwado, sa’an nan fasahar Juncao ta kunshi fannoni guda 2:

Na farko, noman ciyawar Juncao. Wannan ciyawa tana girma cikin matukar sauri, inda ake iya samun ciyayin ton 180 kan gonar kadada daya a duk shekara. Da wadannan ciyayi za a iya kiwon shanu 20. Ban da haka ciyayin na da daraja sosai a fannin kare halittu, ganin yadda nomansu ke iya kyautata yanayin kasa, da magance kwararar hamada.

Sa’an nan fanni na biyu game da fasahar Juncao shi ne, amfani da ciyayin Juncao wajen hada ledar noman laimar kwado, daga baya a dinga noman laimar kwado a kanta. Idan an kwatanta da fasahar gargajiya ta noman laimar kwado kan ice, wannan sabuwar fasaha ta fi samar da laimar kwado, gami da tabbatar da ingancinsu, da kare muhalli.

Wannan fasahar da kasar Sin ta samu a lokacin da take kokarin zamanintar da aikin gona, da rage talauci da raya kauyuka, tana taka rawar gani yanzu a kasashen Afirka, a fannonin samar da abinci, da rage talauci. Misali, wani matashi dan kasar Rwanda mai suna Mushimiyiman Leonidas ya samu damar koyon fasahar Juncao a kasar Sin a shekarar 2013. Bayan da ya kammala horo, ya koma Kigali, inda ya bude wata masana’anta. Zuwa yanzu masana’antarsa tana iya samar da ledar noman laimar kwado dubu 30 a duk wata, gami da laimar kwado kilo 600 a kowane mako. Yanzu a kasar Rwanda akwai iyalai fiye da 4000 da suke noman laimar kwado, sha’anin da ya ba mutane fiye da dubu 30 ayyukan yi.

Don nagartacciyar fasahar Juncao ta amfani karin mutane, kasar Sin ta dade tana kokarin yayata ta a duniya. Zuwa farkon shekarar bana, kasar Sin ta shirya kwasa-kwasai har guda 270 na koyar da fasahar Juncao, wadanda suka shafi mutane fiye da dubu goma daga kasashe daban daban. Yanzu haka, ban da Rwanda, an yada fasahar zuwa Najeriya, da Afirka ta Kudu, da Kenya, da Tanzania, da sauran kasashen dake nahiyar Afirka da dama. A cewar Amson Sibanda, jami’in hukumar kula da tattalin arziki da zaman al’umma ta MDD (UNDESA), fasahar Juncao za ta iya taimakawa kokarin cimma burin samun ci gaba mai dorewa na shekarar 2030, gami da yunkurin daidaita matsalar karancin abinci, da ta gurbacewar muhalli, da kuma talauci.

Yaduwar fasahar Juncao ta nuna ra’ayin Sinawa na “koyar da dabararsu maimakon bayar da kyautar kifi”, gami da tunaninta na hadin gwiwa da kasashen Afirka, wato gaskiya, da sahihanci, da kauna, da kuma haifar da hakikanan ci gaba. Duk darajar wata fasaha, idan dai za ta sanya kasashen Afirka samun hakikanin ci gaba, da kyautatuwar rayuwar jama’a, to, kasar Sin za ta yayata ta ba tare da wani jinkiri ba. A ganin Sinawa, wannan shi ne ra’ayi mai dacewa na hulda da abokai. (Bello Wang)