Iran ta ce da makami mai linzami mai gajeran zango aka kashe shugaban Hamas
2024-08-04 16:59:19 CMG Hausa
Dakarun juyin juya halin Musulunci na Iran wato IRGC sun bayyana a jiya Asabar cewa, an kashe shugaban ofishin siyasa na kungiyar Hamas Ismail Haniyeh ne da wani makami mai linzami mai tafiyar gajeren zango da ke dauke da wani kangon yaki mai nauyin kilogiram 7.
Sanarwar ta IRGC ta ce, Isra'ila ce ta tsara harin ta'addanci tare da taimakon gwamnatin kasar Amurka.
Kungiyar ta Hamas ta fada a ranar Asabar cewa, shugabannin kungiyar da cibiyoyin tuntuba sun fara shawarwari tsakaninsu domin zabar sabon shugaban kungiyar.
Wata sanarwar da kungiyar Hamas ta fitar ta ce, an sha kashe shugabanninta shekaru da dama a baya, amma kungiyar ta kan gaggauta zabar wadanda ke maye gurbinsu kamar yadda tsarin kungiyar ya tanada.
Sanarwar ta kara da cewa, hukumomin zartarwar kungiyar da Shura wato babban kwamitin shawarwari, suna ci gaba da gudanar da ayyukansu, kuma za su bayyana sakamakon shawarar da suka yi da zarar sun kammala. (Yahaya)