Zheng Qinwen ta lashe lambar zinari a wasan tennis na mata na gasar wasannin Olympics ta Paris
2024-08-04 16:56:56 CMG Hausa
An gudanar da wasan karshe na tennis na mata ta gasar wasannin Olympics ta Paris a jiya, inda ‘yar wasan kasar Sin Zheng Qinwen ta doke ta kasar Croatia Donna Vekic, kuma ta lashe lambar yabo ta zinari, kana wannan ne karo na farko da Sin ta samu lambar zinari a wasan tennis na gasar wasannin Olympics. Kana Zheng ta kasance ‘yar wasa ta farko ta nahiyar Asia da ta cimma wannan matsayi a gasar wasannin Olympics.
Zheng Qinwen ta zama matsayi na 6 a jerin sunayen ‘yan wasa mata masu halartar wasan a gasar wasannin Olympics a wannan karo. Kafin wannan, lambar yabo mafi kyau da Zheng ta taba samu ita ce matsayi na biyu a gasar wasan tennis ta Australia Open ta shekarar 2024. A gasar wasannin Olympics ta Paris a wannan karo, ta taba yin wasa har na tsawon awoyi fiye da uku sau biyu a cikin yanayi mai tsananin zafi a kwanaki biyu a jere, a karshe dai ta samu nasara. Ban da wannan kuma, ta doke ‘yar wasan kasar Poland Iga Swiatek a wasan kusa da na karshe, wadda take matsayin farko a duniya.
Ya zuwa yanzu, kasar Sin ta samu lambar zinari daya da ta azurfa daya a wasan tennis a gasar wasannin Olympics ta Paris, hakan ya rubuta sabon babi a tarihin wasannin kasar Sin. (Zainab Zhang)