logo

HAUSA

Akalla mutane 23 ne suka mutu a wani harin da dakarun RSF suka kai a El Fasher

2024-08-04 16:33:46 CMG Hausa

Mashahurin kwamitin gwagwarmaya a kasar Sudan ya bayyana a jiya Asabar cewa, akalla mutane 23 ne suka mutu yayin da wasu da dama suka jikkata sakamakon wani harin bindigogi da dakarun sa kai na RSF suka kai a El Fasher, babban birnin jihar Darfur ta Arewa.

Bisa bayanan da aka samu ya zuwa yanzu, akalla 'yan kasar 23 ne suka mutu, wasu 60 kuma suka jikkata sakamakon bude wutan da RSF ta yi da gangan, a cewar wata sanarwar da majalisar gudanarwa na kwamitin gwagwarmayar a El Fasher, wata kungiya mai zaman kanta ta wallafa a shafinta na Facebook.

Sanarwar ta kara da cewa, a ci gaba da kai hare-hare kan cibiyoyin kiwon lafiya a jihar, a ranar Asabar din, dakarun RSF sun kai hari cibiyar kula da lafiya ta Tambasi da ke kudancin El Fasher.

Zuwa wannan lokaci dai ba a iya samun hukumomin gwamnati a El Fasher don jin ta bakinsu ba, yayin da RSF din ba su ce komai ba kan lamarin.

Tun daga ranar 10 ga watan Mayu har zuwa yanzu ake ta gwabza kazamin fada a El Fasher tsakanin dakarun sojin Sudan (SAF) da na RSF. (Yahaya)