Gwamnatin tarayyar Najeriya ta bayyana takaicin ta a game da abubuwan dake faruwa mara dadi a kasar sakamakon zanga-zanga
2024-08-03 16:08:33 CMG Hausa
Gwamnatin tarayyar Najeriya ta bayyana takaicin ta kan yadda zanga-zangar da al`ummar kasar suka fara ranar Alhamis ta janyo babbar asara a dukiyoyin gwamnati da na daidaikun al`umma a wasu jahohin kasar.
Ministan yada labarai da wayar da kan jama`a na kasar Alhaji Muhammed idris ne ya bayyana hakan jiya Jumma’a 2 ga wata a a birnin Abuja lokacin da ya amsa tambayoyin manema labarai a game da abubuwan da suka biyo bayan zanga zangar.
Daga tarayyar Najeriya wakilin mu Garba Abdullahi Bagwai ya aiko mana da rahoto.
Alhaji Muhammed idris ya ce tun da farko abin da gwamnati ta guda ke nan shi ya sa ta dauki lokaci wajen fadakar da al`umma a game da rashin alfanun zanga-zanga a wannan yanayi da ake ciki.
Ya ce hakika Najeriya kasa ce da demokuradiyya ke aiki, inda kowanne dan kasa yake da ikon fitowa domin gabatar da kokensa ga gwamnati, amma duk da haka gwamnati ta hango mummunar aniyar wasu marasa son cigaban kasa wajen fakewa da yanayin zanga-zangar domin haifar da hargitsi da satar kayayyakin al`umma tare kuma da lalata kaddarorin gwamnati.
Ministan yada labaran ya cigaba da cewa tun da farko shugaban kasa ya sanar da matasan da suka shirya zanga-zangar cewa ya fahimci matsalolin su, kuma ya san al`umma na cikin halin kunchi, amma a ba shi lokaci komai zai daidaita.
“Mun ga abubuwan da suka fara a Kano da Kaduna da Borno da Jigawa da jihar Niger da Sokoto da wasu sassan kasa, abun takaici ne matuka mun yi tunanin hakan zai iya faruwa, na sha fada a baya cewa wasu marasa kishin kasa `yan ta`adda zasu karbe ragamar zanga-zangar, wannan ya sanya tun da farko aka bukaci wadanda suka shirya zanga-zangar da su fito a san su domin a zauna a teburin sulhu domin kuwa sulhu wani bangare ne na demokradiyya”.(Garba Abdullahi Bagwai)