logo

HAUSA

Xi Jinping ya taya Tô Lâm murnar zama sabon babban sakataren kwamitin kolin jam’iyyar kwaminis ta kasar Vietnam

2024-08-03 16:33:38 CMG Hausa

Yau Asabar 3 ga wata babban sakataren kwamitin kolin jam’iyyar kwaminis ta kasar Sin Xi Jinping, ya aike da sako zuwa ga Tô Lâm, don taya shi murnar zama sabon babban sakataren kwamitin kolin jam’iyyar kwaminis ta kasar Vietnam.

A cikin sakon nasa, Xi ya ce, Sin da Vietnam kasashe ne masu bin tsarin gurguzu dake makwabtaka da juna. Yana kuma mai fatan yin kokari tare da Tô Lâm, don ci gaba da raya al’ummomin kasashen biyu masu kyakkyawar makoma ta bai daya, da habaka dadadden zumunci, da karfafa samun fahimtar juna ta fannin siyasa, da ci gaba da zurfafa mu’amala, da fadada hadin-gwiwa, don samar da karin alfanu ga al’ummomin kasashen biyu, tare da bada gudummawa ga sha’anin wanzar da zaman lafiya, da samar da ci gaba ga daukacin al’umma.

Da safiyar Asabar din nan ne aka yi cikakken zama na 13, na kwamitin kolin jam’iyyar kwaminis ta kasar Vietnam a Hà Nội, kuma a wajen taron manema labarai na bayan taron, an sanar da cewa, Tô Lâm ya zama sabon babban sakataren kwamitin kolin jam’iyyar kwaminis ta kasar. (Murtala Zhang)