An binne shugaban Hamas Ismail Haniyeh a Qatar
2024-08-03 17:33:09 CMG Hausa
A jiya Juma’a ne aka binne shugaban Hamas Ismail Haniyeh a kasar Qatar, bayan hallaka shi a birnin Tehran fadar mulkin kasar Iran. To sai dai kuma wanda ake zaton zai maye gurbin sa ya shaidawa wadanda suka halarci jana’izar, cewa kisan jagoran na su ba abun da zai haifar sai karfafa gwiwar Palasdinawa wajen ci gaba da gagwarmaya da Isra’ila.
Kisan Haniyeh na cikin kashe kashen manyan kusoshin Hamas na baya bayan nan da ya auku, yayin da yaki tsakanin Hamas da Isra’ila a Gaza ke daf da shiga wata na 11, kuma ake nuna damuwar yiwuwar fadan zai yadu zuwa karin sassan gabas ta tsakiya.
Hamas da Iran na ci gaba da zargin Isra’ila da kisan Haniyeh, sun kuma sha alwashin mayar da martanin ramuwar gayya. To sai dai a nata bangaren, Isra’ila ba ta bayyana ko ita ce ta hallaka shugaban na Hamas ko a’a ba. (Saminu Alhassan)