A yau Nijar take bikin samun ‘yanci ko sallar shuka itace
2024-08-03 20:12:55 CMG Hausa
A jamhuriyar Nijar, a yau ne ‘yan kasar Nijar suke bikin sallar samun ‘yancin kai ko sallar shuka itace, 3 ga watan Augustan shekarar 1960 zuwa 3 ga watan Augustan shekarar 2024, shekaru 64 ke nan, da kasar ta samu ‘yancin kai. « Babbar ganuwar itatuwa a Nijar, mu shiga aiki », shi ne taken da aka rike ta bikin ranar yau 3 ga watan Augustan shekarar 2024.
Daga birnin Yamai, abokin aikin mu Mamane Ada ya aiko mana da wannan rahoto.
Wannan shekara, bikin karo na 49, zai gudana a cikin kebabben dajin Guesselbodi, na jahar Kollo da ke cikin yankin Tillabery.
Tun a shekarar 1975, wannan biki aka kebe shi ga ayyukan shuka itatuwa a dukkan fadin kasar Nijar domin yaki da hamada, kare muhallin halittu da kuma kokarin dakatar da zaizayewar kasa.
Sallar shuka itace ta wannan karon na da muhimmanci sosai, mu tunatar da cewa Nijar na babban shirin ganuwar itatuwa da ya hada da wasu kasashen Afrika, kamar da Burkina Faso, Djibouti, Eritrea, Ethiopia, Mali, Mauritania, Nigeria, Senegal, Sudan da Cadi.
A Nijar, wannan babbar ganuwar itatuwa masu launin kore za ta ratsa yankunan Nijar guda 8, kuma ta shafi kananan hukumomi 228 bisa kananan hukumomi 266 da kasar Nijar ta ke da su.
Mamane Ada, sashen hausa na CMG daga Yamai a jamhuriyyar Nijar.