logo

HAUSA

Mataimakin firaministan Sin ya jaddada muhimmancin kare jama’a daga fadawa hadurra yayin aikin shawo kan ambaliya

2024-08-03 17:46:25 CMG Hausa

Mataimakin firaministan kasar Sin Zhang Guoqing, ya jaddada muhimmancin kare jama’a daga fadawa hadurra, da tabbatar da samarwa al’umma kayayyakin bukatun yau da kullum, yayin da ake gudanar da aikin shawo kan ambaliyar ruwa, da takaita asara sakamakon aukuwar ibtila’in.

Zhang, ya yi tsokacin ne lokacin da ya ziyarci iyalai da ambaliyar ruwa ta shafa, tare da duba ayyukan shawo kan ambaliyar a lardin Jilin na arewa maso gabashin kasar Sin a ranaikun Alhamis da Juma’a.

Ya ce ya wajaba kwararru su kasance kan gaba, a kuma yi amfani da kayayyakin aiki irin su jirage marasa matuka, da na’urorin sadarwa masu alaka da aikin, domin gaggauta gano hadurra, da tabbatar da tsaron ababen more rayuwa, irin su jinga da ma’adanar ruwa.

Kaza lika, mista Zhang ya yi kira da a kara azamar kwashe al’ummun da ambaliyar ruwan ta shafi matsugunnansu, da gaggauta kare asarar rayuka, kana a sanya ido ga wuraren da ke fuskantar hadarin samun mamakon ruwan sama da ambaliya, da karfafa samar da kudade, da kayan tallafi ga yankunan dake fuskantar matsalar.  (Saminu Alhassan)