logo

HAUSA

'Yan wasan kasar Sin suna kara lashe lambobin yabo a gasar Olympics ta birnin Paris

2024-08-03 17:29:08 CMG Hausa

Yayin da gasar Olympics ta birnin Paris ta shiga mako guda, a jiya Juma’a 2 ga watan nan, ‘yan wasan tawagar kasar Sin dake fafata a gasar na kara lashe lambobin yabo a wasanni daban daban, inda ya zuwa jiyan lambobin da suka lashe suka kai 31.

Huang Yaqiong, da Zheng Ziwei sun lashe lambar zinari a wasan kwallon badminton ta hadakar maza da mata. Yayin da Wang Xinyu da Zhang Zhizhen suka lashe lambar azurfa a gasar kwallon tennis ta hadaka. A gasar ta kwallon tennis, ‘yan wasan kasar Czechia Katerina Siniakova da Tomas Machac ne suka lashe lambar zinari, yayin da ‘yan wasan kasar Canada Gabriela Dabrowski, da Felix Auger-Aliassime suka lashe lambar tagulla.

Karin ‘yan wasan Sin da suka lashe lambobin yabo sun hada da Huang Yuting da Sheng Minghao, wadanda suka lashe lambar zinari a wasan harbin bindiga daga nisan mita 10 na hadakar ‘yan wasa maza da mata, yayin da su ma Long Daoyi da Wang Zongyuan, suka lashe lambar zinari a gasar alkafura cikin ruwa daga tudun mita 3 na ‘yan wasa biyu tare ajin maza.

A gasar sarrafa jiki kan dankon trampoline kuwa, ‘yan wasan Sin Wang Zisai da Yan Langyu sun yi nasarar lashe lambar azurfa da tagulla a ajin gasar ta maza. A daya bangaren kuma, dan wasan ninkaya na Sin Wang Shun, ya yi nasarar lashe lambar tagulla a gasar ninkaya mai nisan mita 200 ajin daidaikun ‘yan wasa maza.

Ya zuwa yanzu, ‘yan wasan kasar Sin sun lashe lambobin yabo 31 a gasar ta birnin Paris, wadanda suka hada da zinari 13, da azurfa 9 da tagulla 9.  (Saminu Alhassan)