Mukaddashin ministan wajen Iran: Iran za ta dauki matakan kare tsaron kasa
2024-08-02 11:39:31 CMG Hausa
Labarin da aka ruwaito daga kafar yada labarai ta kasar Iran wato IRNA a jiya Alhamis, ya nuna cewa, mukaddashin ministan harkokin wajen kasar Iran Ali Bagheri Kani ya aika wasikar dake dauke da sako ga babban magatakardan MDD, da shugaban kwamitin sulhu na MDD na wannan wata, da kuma babban sakataren kungiyar hadin gwiwa ta Musulunci, inda ya bayyana aniyar kasar Iran na daukar matakai masu dacewa domin kare tsaron kasa.
Cikin wasikarsa, Mista Kani ya yi kira ga gamayyar kasa da kasa da su yi Allah wadai da kisan gillar da aka yi wa shugaban ofishin siyasa na kungiyar gwagwarmaya ta Islama ta Falasdinu (Hamas), Ismail Haniyeh. Ya kuma bukaci a kira taron musamman na kwamitin sulhu na MDD, da taron gaggawa na ministocin kungiyar hadin gwiwa ta Musulunci, inda ya kuma yi kira ga MDD da kungiyar hadin gwiwa ta Musulunci da su dakatar da Isra’ila wajen ci gaba da aikata laifuffuka kan Falasdinawa. (Maryam)