logo

HAUSA

An samu asarar rayuka da kaddarori yayin zanga-zangar gama gari da ’yan Najeriya suka fara jiya Alhamis

2024-08-02 09:45:54 CMG Hausa

Al’ummar Najeriya sun fara gudanar da zanga-zangar nuna adawa da manufofin gwamnatin kasar ta fuskar tattalin arziki da tsaro a jiya 1 ga watan Agusta. An gudanar da zangar-zangar ne a duk fadin jihohin kasar ciki har da Abuja, inda kamar yadda aka tsara za a shafe kwanaki goma ana yi.

Daga tarayyar Najeriya wakilinmu Garba Abdullahi Bagwai ya aiko mana.

 

A birnin Abuja, fadar gwamantin kasar, masu zanga-zanga sun fafata da jami’an tsaro a lokacin da aka bukaci su da su taru a harabar filin taro na Eagles Square domin gudanar da zangar-zangar, kin bin wannan umarni ne jami’an tsaro suka fara amfani da hayaki mai sa hawaye ga masu zanga-zangar, matakin kungiyoyin kare hakkin bil’adama suka yi alawadai.

A jihar Yobe dake arewa maso gabashin Najeriya wasu matasa ne suka yi amfani da zanga-zangar ta jiya Alhamis wajen cinna wuta a wasu manyan motocin hukumar sufuri ta jihar guda 7 sannan kuma sun lalata sakatariyar mulkin karamar hukuma.

A jihar Kano kuma dake arewa maso yammacin Najeriya, wasu bata gari ne suka yi amfani da wannan dama wajen satar kayayyakin jama’a da na gwamnati, sannan kuma mutane biyu sun rasu a lokacin da jami’an tsaro ke kokarin tarwatsa masu zanga-zangar, tun dai a jiyan gwamnan jihar Alhaji Abba Kabir Yusuf ya sanya dokar hana fita na tsawon sa’o’i 24 domin dai tabbatar da doka da oda.

Rahotannin kuma daga jihar River dake shiyyar kudu maso kudancin Najeriya, titunan birnin Fatakwal ne ya kasance babu jama’a sosai, amma kalilan din mutane ne suka sami fitowa dauke da kwalaye dake bayyana damuwarsu ga gwamnati, sannan kuma suna rera wakoki na neman sauki, yayin da wasu magidanta kuma sun leka manyan kwalaye a jikin gidajen su wanda ke nuna cewa suna goyon bayan wannan zanga-zangar, ko da yake dai masu shaguna ba su bude ba gaba daya.

Daga jihar Legos kuwa dake kudu masu yammacin Najeriya masu zanga-zanga ne sun taru ne a dai dai gadar Ikeja daga bisani kuma suka karasa Ojota inda suke tafe suna rera wakoki na neman ’yanci bisa rakiyar jami’an tsaro masu yawan gaske.

An dai samu daukewar ababen hawa a babbar hanyar Lagos zuwa Ibadan da kuma hanyar Alausa.

Sai kuma a jihar Enugu dake kudu maso gabashin Najeriya al’ummar yankin sun gudanar da zanga-zangar su ne ta hanyar zama a gida, wannan ya sanya harkokin kasuwanci sun tsaya cik a babban birnin, sai dai kawai jami’an tsaro ne ke ta sintiri a kan tituna domin dai sanya ido. (Garba Abdullahi Bagwai)