‘Yan sanda: Mutane 16 ne suka mutu yayin da 20 suka jikkata a wata mummunar fashewar bam a Najeriya
2024-08-02 10:08:07 CMG Hausa
‘Yan sanda a Najeriya sun ce a kalla mutane 16 ne suka mutu yayin da wasu 20 suka jikkata bayan wata mummunar fashewar bam da ya auku a kasuwar dare a jihar Borno da ke arewa maso gabashin Najeriya da yammacin Laraba.
Babban jami’in ‘yan sanda Yusuf Lawan ya shaidawa kamfanin dillancin labarai na Xinhua ta wayar tarho a safiyar Alhamis cewa, lamarin ya faru ne biyo bayan tashin bam da ake zargin dan kunar bakin waken Boko Haram ne ya tayar a kasuwar Kawuri da ke karamar hukumar Kondauga a jihar.
Lawan ya ce, nan take aka tura tawagar ‘yan sanda zuwa wurin domin killace wurin daga karin tashin bama-bamai tare da dawo da zaman lafiya.
Bayan aukuwar lamarin, rundunar ‘yan sandan ta sanya dokar hana fita ta sa’o’i 24 a fadin jihar, a cewar Nahum Daso, kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Borno a wata sanarwa ta daban. (Yahaya)