‘Yan sanda: Mutane 4 ne suka mutu, 34 kuma suka jikkata sakamakon fashewar bam a wurin zanga-zanga a arewacin Najeriya
2024-08-02 11:51:06 CMG Hausa
‘Yan sanda Najeriya sun ce a kalla mutane 4 ne suka mutu yayin da wasu 34 kuma suka jikkata, bayan fashewar bam a wurin zanga-zangar tsadar rayuwa a jihar Borno da ke arewa maso gabashin Najeriya a ranar Alhamis.
Da yake zantawa da manema labarai a Abuja, babban birnin tarayyar Najeriya da yammacin jiya Alhamis, Sufeto Janar na ‘yan sandan kasar Kayode Egbetokun, ya ce bam ya tashi a Maiduguri, babban birnin jihar Borno, a yayin zanga-zangar da ta barke a fadin kasar.
Egbetokun ya bayyana cewa, ‘yan sanda sun yi hasashen bata gari za su kutsa cikin wuraren da ake gudanar da zanga-zangar a fadin Najeriya, inda suka tabbatar da rahoton farko da kuma gargadin da hukumomin tsaro suka bayar wanda ya sanar da ‘yan kasar kan hatsarin da ke tafe da zanga-zangar a fadin kasar.
A yayin da yake ba da gargadi ga daukacin rundunonin ‘yan sanda da sauran sassa saboda yadda zanga-zangar ta zama ta tashin hankali, Egbetokun ya tabbatar da an yi barna a jimillar jihohi 8 daga cikin 36 na Najeriya a ranar farko ta zanga-zangar, yana mai zargin ainihin manufar masu zanga-zangar.
A wata tattaunawa ta daban da manema labarai, babban jami’in ‘yan sanda a Borno, Yusuf Lawal, ya ce ana zargin ‘yan kungiyar ta’addancin nan ta Boko Haram da ke da sansani a yankin arewa maso gabashin Najeriya da kuma kasashen yankin tafkin Chadi da kutsawa cikin masu zanga-zanga a ranar Alhamis. (Yahaya)