logo

HAUSA

Xi Jinping ya amsa wasikar ’yan kasuwa na yankin Hong Kong ’yan asalin birnin Ningbo

2024-08-01 11:36:53 CMG Hausa

A kwanakin baya, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya ba da amsa ga wasikar da wasu ’yan kasuwa na yankin Hong Kong ’yan asalin birnin Ningbo na babban yankin kasar Sin ciki har da Bao Peiqing, da Cao Qiyong da sauransu suka rubuta masa.

A cikin sakonsa, shugaba Xi ya yi nuni da cewa, a cikin shekaru da dama da suka gabata, ’yan kasuwa kaka da kakaninku sun kiyaye dabi’arsu na kaunar kasa da garinsu, suna kokarin kafa kamfanoni da aiwatar da ayyukansu, da ba da tallafin kudi ga makarantun garinsu, ta hakan sun ba da gudummawarsu ga raya garinsu da ma kasarsu. Xi yana fatan za su ci gaba da yin amfani da fifikonsu wajen shiga ayyukan kara yin kwaskwarima da bude kofa ga kasashen waje a kasar Sin, da ma samun zamanintarwa irin ta kasar Sin da farfado da al’ummar kasar Sin baki daya. (Zainab Zhang)