Sin ta kashe yuan biliyan 300 a aikin gina tituna a Xizang a tsakanin shekarar 1953-2023
2024-08-01 10:48:36 CMG Hausa
Ofishin yada labarai na gwamnatin jihar Xizang ta kasar Sin ya bayyana a jiya Laraba cewa, gwamnatin tsakiya ta kasar Sin ta kashe yuan biliyan 325.1 kwatankwacin dalar Amurka biliyan 45.6 don gina tituna a jihar Xizang dake kudu maso yammacin kasar Sin daga shekarar 1953 zuwa 2023.
Ofishin ya bayyana a taron manema labarai cewa, jimillar tsayin titunan da aka bude wa zirga-zirgar ababen hawa a birnin Xizang a halin yanzu ta kai kilomita 123,300, tare da shimfidaddun hanyoyin da suka ratsa cikin garuruwa 666 da kauyuka 4,596.
Xizang shi ne yanki daya tilo a matakin larduna a kasar Sin inda gwamnatin tsakiya ta samar da cikakken kudin aikin gina tituna. (Yahaya)