Najeriya ta ce rikicin Rasha da Ukraine na daya daga cikin musabbabin halin matsi da ake ciki a kasar a halin yanzu
2024-08-01 09:23:21 CMG Hausa
Ministan kudi a tarayyar Najeriya Mr Wale Edun ya tabbatar da cewa, shugaba Bola Tinubu ya fahimci halin da ’yan Najeriya ke ciki, inda ya ce, hauhawar farashin kayan abinci al’amari ne da ya shafi duniya baki daya.
Ministan yana magana ne jiya Laraba 31 ga watan jiya a birnin Abuja yayin taron ’yan jaridu na duniya da aka gudanar domin kara fahimtar da al’umma ainihin kokarin da gwamnati ke yi wajen rage masu radadin rayuwa.
Daga tarayyar Najeriya wakilinmu Garba Abdullahi Bagwai ya aiko mana da rahoto.
Taron ’yan jaridun wanda ministocin yada labarai da na kasafin kudi da tsare-tsare da ministan ma’adanai suka sami damar yin bayanin irin nasarorin da gwamnati ta samu a bangarorinsu a cikin shekara guda, ya yi fatan zanga-zangar da za a fara yau din Alhamis za`a yi shi cikin kwanciyar hankali.
Kamar dai yadda ministan kudin ya bayyana tsadar rayuwa da ake ciki ba wai kawai Najeriya abun ya shafa ba, lamari ne da ya shafi duniya baki daya, wanda kuma ya samo asali ne daga yakin dake wakana tsakanin Rasha da Ukraine da kuma wanda ake yi yanzu haka a Sudan.
Ministan kudin haka kuma ya ce, yawan dogaro da Najeriya ke yi wajen shigo da kayayyakin sarrafawa a masana’antu daga kasashen wajen shi ma ya kara jefa kasar cikin tsadar kayayyaki, bayan haka kuma har yanzu duniya ba ta gama murmurewa ba daga tasirin annobar Covid-19.
A kan halin da tattalin arzikin kasar ke ciki kuwa, ministan ya ce, a tsakanin watanni 15, tattalin arzikin Najeriya ya fara farfadowa sosai.
“Yanzu tattalin arzikinmu yana bukasa tun daga farko na wannan shekara. Harkar noma wadda ta kasance ya yi rauni sosai. Lamarin da ya haddasa karancin abinci da kuma tsadarsa, amma yanzu shi ma ya fara dagowa tun daga watannin farko na wannan shekara. Haka kuma bangaren masana’antu da na ma’adanai da na fasahar sadarwa duk suna samun ci gaba kuma suna samar da kafofin aikin yi ga ’yan kasa, kuma za mu yi bakin kokarin ganin ba a sake komawa baya ba.” (Garba Abdullahi Bagwai)