Kamfanin kasar Sin ya mika manyan kayan aiki don taimakawa aikin inganta hanyoyin kasar Ghana
2024-08-01 10:28:12 CMG Hausa
Kamfanin kayayyakin aiki na LiuGong na kasar Sin ya mika wa gwamnatin kasar Ghana manyan kayayyakin aiki 2,200 a jiya Laraba, don tallafawa shirin inganta hanyoyin mota na gundumomi na kasar wato DRIP.
Kayayyakin da gwamnatin kasar Ghana ta saya domin gyaran tituna a
fadin kasar, sun hada da motocin gireda, da buldoza, da injinan hada
kankare, da motocin daukar kaya, da rollers, da motocin tipper, da
tankunan ruwa.
A yayin bikin mika kayayyakin, shugaban kasar Ghana Nana Addo Dankwa Akufo-Addo ya ce aikin ya kasance wani muhimmin ci gaba a kokarin da Ghana ke yi na samar da ababen more rayuwa.
Akufo-Addo ya kara da cewa, "Muna ci gaba da nuna godiya ga hadin gwiwa tsakanin gwamnati da jama'ar Ghana da gwamnati da jama'ar kasar Sin, kuma muna fatan hadin gwiwar ta bunkasa." (Yahaya)