logo

HAUSA

Manzon musamman na Xi Jinping ya halarci bikin rantsar da shugaban Iran

2024-08-01 10:56:07 CMG Hausa

Bisa gayyatar da aka yi masa, a ranar 30 ga wata, manzon musamman na shugaban kasar Sin Xi Jinping, Peng Qinghua ya halarci bikin rantsar da sabon shugaban kasar Iran Masoud Pezeshkian. Sa’an nan, a jiya Laraba, shugaba Pezeshkian ya gana da Peng Qinghua a fadar shugaban kasa.

A yayin ganawarsu, Mista Peng ya mika gaisuwa da fatan alheri da shugaban kasar Sin Xi Jinping ya yi wa shugaba Pezeshkian. Ya ce, shugaba Xi Jinping ya taya shi murnar kama aikin shugabancin kasar Iran. Kuma, kasar Sin tana fatan zurfafa fahimtar siyasa a tsakanin kasashen biyu, da inganta hadin gwiwar dake tsakaninsu a fannoni daban daban yadda ya kamata, domin cimma moriyar juna. Haka kuma, Sin na fatan ciyar da dangantakar abokantaka bisa manyan tsare-tsare a tsakanin kasashen biyu gaba.

A nasa bangare kuma, shugaba Pezeshkian ya ce, sabuwar gwamnatin kasar Iran za ta dukufa wajen zurfafa dangantakar dake tsakaninta da kasar Sin, kuma tana tsayawa tsayin daka wajen goyon bayan kasar Sin kan harkokin kare moriyarta. Kana, za ta halarci shawarar “Ziri daya da hanya daya” da manyan shawarwari guda uku cikin himma da kwazo, domin inganta dangantakar dake tsakanin Iran da Sin zuwa wani sabon matsayi. (Mai Fassara: Maryam Yang)