logo

HAUSA

Shugaban MDD ya bukaci a sassauta rikicin yankin Gabas ta Tsakiya

2024-08-01 09:39:00 CMG Hausa

Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres a ranar Laraba ya yi kira da a daina tashe-tashen hankula a yankin Gabas ta Tsakiya domin samar da zaman lafiya da kwanciyar hankali ga kowa da kowa.

Mai magana da yawun Guterres, Stephen Dujarric a cikin wata sanarwa ya ce, babban sakataren ya yi imanin cewa hare-haren da suka faru a kudancin Beirut da Teheren suna wakiltar wani mummunan tashin hankali a daidai lokacin da ya kamata a mai da hankali kan tsagaita wuta a Gaza, da sakin dukkan Isra’ilawa da ake rike da su, da kara ayyukan agajin jin kai ga Falasdinawa a Gaza da kuma dawo da kwanciyar hankali a Lebanon da sauran sassan da ke tsakanin Lebanon da Isra’ila. "Maimakon haka, abin da muke gani shi ne kokarin dakushe wadannan manufofin," a cewar Dujarric. (Yahaya)