logo

HAUSA

Wang Yi ya jaddada muhimmancin diflomasiyya tsakanin mabambantan al’ummu

2024-08-01 21:04:40 CMG Hausa

Ministan harkokin wajen kasar Sin Wang Yi, ya jaddada muhimmancin diflomasiyya tsakanin mabanbantan al’ummu, yana mai kira ga kungiyar sada zumunta da kasashen waje ta al’ummar Sinawa ko CPAFFC, da ta kara azamar shiga gamammiyar musaya, a matakai daban daban, daga dukkanin fannoni tsakanin ta da kasashen waje.

Wang, ya yi wannan kira ne a Alhamis din nan, yayin bikin bude babban taron kungiyar ta CPAFFC karo na 11, yana mai cewa a bana kungiyar ke cika shekaru 70 da kaddamarwa, kuma ita ma a nata bangare jam’iyyar kwaminis ta kasar Sin(JKS), tana dora muhimmancin gaske ga bunkasa diflomasiyya tsakanin mabanbantan al’ummu.

Daga nan sai ya jaddada cewa, ya kamata CPAFFC ta taka cikakkiyar rawar gani a fannin wanzar da diflomasiyya tsakanin mabanbantan al’ummu, da bunkasa kawance tsakanin Sinawa da al’ummun sauran kasashen duniya, da yayata hadin gwiwar cimma moriyar juna, da kara kyautata gudummawar gina daukacin kasar Sin.  (Saminu Alhassan)