logo

HAUSA

Ma’aikatar harkokin wajen Sin: Zargin da aka yiwa kasar Sin na barazana ga Intanet yana kunshe da wata mummunar manufa

2024-08-01 21:29:15 CMG Hausa

Rahotannin baya-bayan nan sun ruwaito cewa, kasar Jamus ta fito fili ta zargi kasar Sin, dake cewa wai tana haifar da barazana ga harkokin yanar gizo ko Intanet. Game da hakan, mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Lin Jian, ya maida martani kan wannan batu a taron manema labarai da aka yi yau Alhamis 1 ga wata, inda ya ce, kasarsa na adawa da irin wannan matakin siyasa da aka dauka, don rura wutar nuna kyama ga kasar Sin.

Kakakin ya ce, a kwanan nan, akwai wasu ’yan siyasa da kafafen yada labarai na kasashen yammacin duniya, da suka gabatar da bayanai na karya, tare da kikiro wasu labaran bogi da gangan, inda suka ce kasar Sin na haifar da barazana ga Intanet. Babu shakka, makasudinsu ba wai inganta tsaron Intanet ba ne.

Kaza lika, kakakin ya jaddada cewa, Sin ta bukaci kasar Jamus da ta tsaya ga ra’ayin kanta, ta yi fatali da yin fito-na-fito, da ra’ayin yakin cacar baka, don kiyaye zaman lafiya da tsaro a bangaren Intanet, ta hanyar gudanar da shawarwari, da karfafa hadin-gwiwa tare da sauran sassan kasa da kasa. (Murtala Zhang)