logo

HAUSA

An rantasar da Masoud Pezeshkian a matsayin shugaban Iran

2024-07-31 10:35:38 CMG Hausa

 

An rantsar da zababben shugaban kasar Iran Masoud Pezeshkian a hukumance a majalisar dokokin kasar Iran da yammacin jiya Talata.

A cikin jawabin da ya fitar a ranar, Pezeshkian ya yi alkawari cewa, sabuwar gwamnatin kasar za ta inganta ci gaba mai dorewa, da karfafa tattalin arziki da kuma inganta ingancin rayuwar al’ummar kasar, a sa’i daya kuma, za ta himmatu wajen kiyaye mutunci da moriyar kasar, kuma za ta yi kokarin cimma matsaya daya tare da dukkanin jam’iyyun siyasa a kasar.

Bugu da kari, Pezeshkian ya yi kira ga kasa da kasa da ta yi hadin gwiwa da Iran, don warware kalubalolin yankuna da na duniya, kuma ya bayyana cewa, yin mu’ammala da kasashen duniya bisa manufar da ta dace zai zama tushen gudanar da harkokin diplomassiya na sabuwar gwamnatin Iran. (Safiyah Ma)