An tanadi ’yan sanda dubu 5 a jihar Kebbi domin sanya ido kan masu zanga-zangar da za a fara daga gobe
2024-07-31 11:51:32 CMG Hausa
Rundunar ’yan sandan jihar Kebbi ta yi gargadin cewa ba za ta lamunci lalata kaddarorin gwamnati da na jama’a ma ba yayin zangar-zangar gama gari da ake tunanin farawa daga gobe Alhamis a jihar.
Kwamashinan ’yan sandan jihar Bello Sani ne ya yi gargadin hakan ranar Talata 30 ga wata a harabar hedikwatar rundunar dake birnin Kebbi lokacin da yake jawabi ga jami’an ’yan sandan dake rundunar.
Daga tarayyar Najeriya wakilinmu Garba Abdullahi Bagwai ya aiko mana da rahoto.
Kwamashinan ’yan sandan na jihar ta Kebbi ya ce, domin ganin cewa an gudanar da zanga-zangar cikin lumana, rundunar ta tanadi ’yan sanda har dubu biyar.
Ya ce, duk da dai cewar kowa yana da ’yancin bayyana damuwarsa ta hanyar zanga-zanga cikin lumana, amma dai ba za a amince da amfani da wannan dama ba wajen daka wawa kan dukiyar jama’a.
A saboda haka kwamishinan ’yan sandan ya yi kira ga jagororin shirya zanga-zangar da su sanar da rundunar hanyoyin da za su bi da kuma dandalin da za su taru da kuma adadin sa’o’in da za su shafe suna zanga-zangar kana kuma da adireshin jagororin domin dai kada a bari wasu bata gari su yi amfani da wannan damar.
“Dukkan jami’an hukumomin tsaro dake jihar ba za su yi wata-wata ba wajen daukar mataki a kan duk wani gungun mutane da suka yi yunkurin kawo cikas ga yanayin zaman lafiyar al’umma a jihar ta Kebbi.”
Kwamishinan ’yan sandan na jihar Kebbi ya kuma gana da sauran shugabannin hukumomin tsaron dake jihar da sarakuna da shugabannin addinai da na kungiyoyi daban daban don ganin zanga-zangar ta gudana cikin natsuwa. (Garba Abdullahi Bagwai)