logo

HAUSA

Kuri'ar jin ra'ayi ta CGTN: Kashi 81.69 cikin dari na masu bayyana ra'ayoyinsu sun nuna damuwa matuka game da karfafa alakar soji tsakanin Japan da Amurka

2024-07-31 14:23:09 CMG Hausa

Kwanan nan, Japan da Amurka sun fitar da sanarwa tare, bayan taron kwamitin ba da shawara kan harkokin tsaro a Tokyo, cewar kasashen biyu sun amince su kara karfafa hadin gwiwar soji ta hanyar inganta karfi da ikon sojojin Amurka dake Japan.

Dangane da batun, a wani binciken da kafar CGTN ta gudanar ta kafar yanar gizo, kashi 81.69 cikin 100 na masu bayyana ra'ayoyinsu sun yi imanin cewa, ci gaban da Amurka da Japan ke yi da hada kai don kafa kebabbun kungiyoyi, wata sabuwar barazana ce da za ta kawo cikas ga zaman lafiya da kwanciyar hankali a yankin, wanda ya cancanci sa ido sosai daga kasashen duniya.

Wannan kuri'ar jin ra'ayi da CGTN ya wallafa a cikin harsunan Turanci, Sifaniyanci, Faransanci, Larabci da Rashanci, ya samu mutane 7,254 wadanda suka bayyana ra'ayoyinsu cikin sa'o'i 24. (Yahaya)