logo

HAUSA

Wakilin Sin: Dage takunkumin hana shigo da makamai zai taimakawa gwamnatocin Afirka ta Tsakiya wajen kara karfin tsaro

2024-07-31 11:48:15 CMG Hausa

 

Mataimakin zaunannen wakilin kasar Sin a MDD, Dai Bing, ya bayyana a cikin jawabinsa bayan da kwamitin sulhu ya kada kuri'ar amincewa da kudurin soke takunkumin da aka yi wa Afirka ta Tsakiya jiya Talata, ya ce kwamitin sulhun ya zartas da kudurin a wannan rana na dage takunkumin hana shigar da makamai da aka kakkaba wa Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya, wanda a aikace ke nuni da tallafawa gwamnatin Afirka ta Tsakiya wajen karfafa matakan tsaro da kuma inganta zaman lafiya.

Dai Bing ya kara da cewa, kasar Sin tana goyon bayan kwamitin sulhu da ya ci gaba da mutunta da kula da damuwar kasar Afirka ta tsakiya, da daukar karin matakai da wuri bisa yanayin ci gaba da bukatun halin da ake ciki, da yin nazari, da daidaitawa, da kuma dage takunkumai da ba su dace ba, ta yadda za a cimma muradu masu amfani don tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali da ci gaba da kuma wadata a kasar Afirka ta Tsakiya da shiyyar inda kasar take. (Safiyah Ma)