An kashe shugaban kungiyar Hamas a birnin Tehran na kasar Iran
2024-07-31 11:51:49 CMG Hausa
Ofishin watsa labarai na rundunar sojan kasar Iran ya sanar a yau Laraba cewa, shugaban ofishin siyasa na kungiyar gwagwarmaya ta Islama ta Falasdinu (Hamas), Ismail Haniyeh, ya rasa ransa, tare da wani mai gadinsa, sakamakon harin da aka kai musu a birnin Tehran, fadar mulkin kasar Iran. Ban da haka, an ce har yanzu ana kokarin bin bahasin harin da aka kaddamar, kuma za a gabatar da sakamako daga bisani. (Bello Wang)