Sojojin Mali sun tabbatar da mutuwar sojoji bayan wani kazamin fada da kungiyoyi masu makamai da ke arewacin kasar
2024-07-31 10:47:39 CMG Hausa
Rundunar sojojin kasar Mali ta tabbatar, a ranar Litinin 29 zuwa ranar Talata 30 ga watan Julin shekarar 2024 da mutuwar wani adadin sojoji bayan wani kazamin fada a makon da ya gabata a arewacin kasar a Tinzaouatene kusa da iyaka da kasar Aljeriya tare da gungun kungiyoyin ’yan ta’adda, a cikin wata sanarwa.
Daga birnin Yamai, abokin aikimu Mamane Ada ya aiko mana da wannan rahoto.
Wani gungun mayaka na kusa da dakarun Wagner ya amince da wannan sanarwa ta sojojin Mali, na cewa sojojin Mali sun rasa dakarunsu a karshen makon da ya gabata a cikin wani fadan da ya barke a arewacin kasar Mali mai iyaka da kasar Aljeriya.
Dakarun FAMA sun shiga tsaka mai wuya a lokacin kungiyoyin ’yan ta’adda dake yankin Sahel suka yi musu zobenya, inda kazamin fada ya barke a tsawon sa’o’i kafin zuwan sojojin da suka dafa baya, a cewar sanarwar FAMA. “Juriya da nacewar sojojinmu sun taimaka wajen kaucewar asasar sojoji da kayan soja,” in ji hedkwatar rundunar sojojin Mali a cikin wata sanarwar da aka karanto ta gidan talabijin na kasar Mali.
Daga ranar 22 zuwa 27 ga watan Julin shekarar 2024 ne, sojojin FAMA na kasar Mali tare da rakiyar dakarun Wagner sun yi bata kashi tsakaninsu mayakan CMA da ke neman ’yancin yankin Azawad tare da na JNIM reshen Al-Qaida a yankin Sahel.
Sai dai sanarwar sojojin Mali ba ta ambato yawan sojojin da suka mutu ba a yayin wannan kazamin fada, amma wasu rahotonni na maganar mutuwar sojojin Wagner 50 da sojojin Mali 10. Sai dai babu wata majiyar da tabbatar da mutuwar wadannan sojoji.
Mamane Ada, sashen hausa na CMG daga Yamai a jamhuriyyar Nijar