logo

HAUSA

Kasar Sin na kokarin tabbatar da zaman lafiya a yankin Gabas Ta Tsakiya

2024-07-31 07:30:41 CMG Hausa

Rikicin Falasdinu da Isra’ila batu ne da ya ki ci ya ki cinyewa, amma rikicin baya-bayan nan ya haddasa matsalar jin kai da ba a taba ganin irinta ba. Wanda kawo yanzu an rasa rayukan mutane kimanin 40,000 mafi yawansu fararen hula, yayin da sama da miliyan 2.3 suka rasa matsugunansu. Sulhunta bangarorin Falasdinawa 14 musamman Hamas da Fatah wato manyan kungiyoyi biyu mafi tasiri a yankin Falasdinu da suka kasance masu adawa da juna tun bayan barkewar rikici a shekara ta 2006, bayan da kungiyar Hamas ta karbe ikon Gaza zai zama wani muhimmin sauyi a dangantakar cikin gidan Falasdinu. Tun a baya an yi ta neman sulhu tsakanin bangarorin biyu amma ba a samu nasara ba. Yayin da Isra'ila da kawayenta ciki har da Amurka suke tattauna kan wanda zai iya jagorantar yankin bayan an kawo karshen yaki a yankin da ya hargitsa Gabas ta Tsakiya.  

Kasar Sin ta tsaya tsayin daka wajen ganin an warware matsalar Falasdinu da Isra’ila ta hanyar tattaunawa tare da yin kira da kakkausar murya kan samar da kasar Falasdinu mai cin gashin kanta, ba ta tsaya nan, ta yi kokarin sassanta bangarorin Falasdinawa da suka dade suna gaba da juna bisa sanin cewa sai bango ya tsage kadangare ke samun mafaka. Sakamakon wannan yunkuri shi ne “Yarjejeniyar Beijing” wanda a karon farko bangarorin Falasdinawa 14 suka amince da rattaba hannu kan yarjejeniyar da za ta dinke barakar cikin gida tare da kawo karshen rarrabuwar kawuna da baiwa Falasdinawa damar mallakar yankinsu bayan yakin, don tabbatar da zaman lafiya a yankin Gabas ta Tsakiya.

Wang Yi ya bayyana cewa, bala'in dake faruwa a zirin Gaza, wani kira ne ga duniya don ta farka, kazalika tsawon lokacin mamayar yankunan Falasdinu, wani lamari ne da bai kamata a yi watsi da shi ba, kuma ya kamata a ce an dade ana kishin Falasdinawa game da tabbatar da samun 'yantacciyar kasa.  Bai kamata a bar zaluncin da aka yi wa Falasdinawa a tarihi ya ci gaba ba tare da an yi gyara saboda makomarta ba. (Sanusi Chen, Saminu Alhassan, Mohammed Yahaya)