logo

HAUSA

Bankin duniya ya amince baiwa Nijar tallafin kudi na dalar Amurka miliyan guda domin zamanintar da noma da kiwo

2024-07-31 11:53:14 CMG Hausa

A jamhuriyyar Nijar, bankin duniya ya amince zuba kudin tallafi na dalar Amurka miliyan guda domin zamanintar da noma da kiwo.

Bikin rattaba hannu ya gudana ranar Litinin din da ta gabata a birnin Yamai tsakanin faministan Nijar Ali Mahamane Lamine Zeine da mataimakin shugaban bankin duniya na shiyyar Afrika, Ousmane Diagana.

Daga birnin Yamai, abokin aikinmu Mamane Ada ya aiko mana da wannan rahoto. 

 

Wannan shiri zai shafi batun zamanintar da muhimman bangarorin noma da na kiwo, bisa amincewa da wata manufar kusanta da ta kunshi matakai uku tare da wakiltar damammakin karfafa karfin hukumomin ci gaba a cikin dogon lokaci da gajeren lokaci, da zuba kudin da suka kai dalar Amurka miliyan guda kimanin fiye da miliyan 600 na kudin Sefa, in ji mataimakin shugaban bankin duniya shiyyar Afrika.

Wannan shiri, na farko irinsa da al’ummar kasar Nijar za ta amfana, ya kasance wani kalubale da ya kamata a cimma, da kuma ya kamata a tabbatar da shi cikin gaggawa, in ji faraministan Nijar Ali Mahamane Lamine Zeine a albarkacin wannan bikin sanya hannu.

Mamane Ada, sashen hausa na CMG daga Yamai a jamhuriyyar Nijar.