logo

HAUSA

Gwamnatin Najeriya ta yi kira da a yi watsi da zanga-zangar da aka yi shirin gudanarwa a kasar

2024-07-31 09:50:22 CMG Hausa

A kokarin da ta ke yi na kaucewa mummunar sakamakon zanga-zangar da ake shirin yi a fadin kasar a wannan mako, gwamnatin Najeriya ta yi kira da a kwantar da hankula, tare da yin kira ga matasa da su ajiye batun zanga-zangar tare da samar da damar tattaunawa don za su iya gabatar da korafe-korafensu.

A ranar Alhamins ne dai matasa za su fara zanga-zanga a fadin kasar da ta fi kowace yawan al'umma a nahiyar Afirka, inda masu fafutuka suka yi kira ga gwamnati da ta magance matsalolin tattalin arziki da ake fama da su a cikin mawuyacin halin tsadar rayuwa.

Ministan yada labarai da wayar da kan jama'a Mohammed Idris ya shaidawa manema labarai a ranar Litinin a Abuja, babban birnin kasar cewa, duk da cewa gwamnati ba ta adawa da gudanar da zanga-zangar lumana a matsayin 'yancin dimokradiyya na kowane dan Najeriya, yana kira ga matasa da su yi watsi da shirin. 

Yayin da ya ke ba da tarihin zanga-zangar da aka yi a kasar, Idris ya ce akwai yiwuwar "bata gari" za su karbe wannan zanga-zangar da aka shirya yi a fadin kasar kuma ta koma tashin hankali. (Yahaya)