logo

HAUSA

Xi Jinping ya jaddada muhimmancin bunkasa ginin jam’iyya a dukkanin matakai

2024-07-31 22:08:18 CMG Hausa

Shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya yi kira ga sassan kwamitin koli na JKS, da na gwamnatin kasar da su bunkasa ginin jam’iyyar a dukkanin matakai, da zama misali na nazari da aiwatar da ginshikan ka’idojin da aka fitar yayin cikakken zama taro na uku na kwamitin kolin JKS na 20.

Cikin wani umarni da ya gabatar, shugaba Xi ya ce kamata ya yi sassan kwamitin koli na JKS, da na gwamnatin kasar su jagoranci nazari, da aiwatar da ginshikan ka’idojin da aka fitar yayin cikakken zama taro na uku na kwamitin kolin JKS na 20.

Kaza lika, ya ce nazari da aiwatar da ka’idojin, muhimmin aiki ne na siyasa da ya rataya a wuyan daukacin jam’iyyar da kasar a wannan gaba da ma a nan gaba.   (Saminu Alhassan)