Me ya kawo matasa zuwa yankin Xizang na kasar Sin?
2024-07-30 10:37:35 CMG Hausa
A shekarun baya bayan nan, mahaifin wata daliba mai suna Tsomo ’yar kabilar Zang ya kafa gandun noman wani nau’in kayan maganin da ake kira Linzhi, a kauyen Xueka dake yankin Xizang na kasar Sin. A shekarar 2018, Tsomo ta gama karatu a jami’ar dake birnin Beijing, ta koma gida. Daga bisani ta yi amfani da ilimin da ta samu wajen raya sha’anin noman Linzhi mai launin fari. Zuwa yanzu, ta zama manaja mai kula da ma’aikata, da aikin sayar da kaya ta yanar gizo, ta hakan ta shigar da sabbin fasahohi da tunani cikin harkokin gandunsu, da taimakawa mahaifinta a kokarinsa na fitar da sauran mazauna wurin daga kangin talauci da wadatar da su.
Labarin Tsomo ya nuna sauyawar yanayin zaman rayuwar matasan yankin Xizang a shekarun nan. Ta haka za mu iya ganin cewa, tabbatar da jin dadin rayuwar jama’a yana da matukar muhimmanci, idan ana son kare hakkin dan Adam. (Zainab Zhang)