logo

HAUSA

Gwamnatin Najeriya za ta fara sayarwa al’ummar kasar shinkafa a kan farashin naira dubu 40 ga kowane kilo 50

2024-07-30 10:26:15 CMG Hausa

Gwamnatin tarayyar Najeriya ta fara raba karin manyan motoci goma na dako kaya dauke da buhunan shinkafa mai nauyin kilo 50 ga kowace jiha, inda za a rinka sayarwa jama’a a farashin naira dubu 40 ga kowane buhu daya.

Gwamnatin ta tabbatar da hakan ne jiya Litinin a birnin Abuja yayin taron majalissar zartaswa ta kasa da aka gudanar karkashin jagorancin shugaba Bola Ahmed Tinubu, tuni ma dai aka samar da cibiyoyi na musamman a kowace jiha da jama’a za su je domin sayen kayan.

Daga tarayyar Najeriya wakilinmu Garba Abdullahi Bagwai ya aiko mana da rahoto.

 

Majalissar zartarwar ta Najeriya ta bayyana cewa, a ganinta babu wata hujja da jama’a za su shiga zanga-zanga kasancewar dai kusan da yawa daga cikin bukatun masu shirya zanga-zangar, gwamnati ta rigaya ta shawo kan su.

A lokacin da yake yi wa manema labarai karin haske game da abubuwan da taro na majalissar zartarwar ya tattauna, ministan yada labarai da wayar da kan jama’a na kasar Alhaji Muhammad Idris ya ce, karin motoci goman na shinkafa da aka baiwa jihohi daya ne daga cikin matakan saukaka rayuwa ga ’yan kasa, inda ya ce, a zaman da majalissar ta yi a kwanakin baya ta sanar da aikewa jihohin motoci 20 na shinkafa kowanen su domin rabawa ga masu karamin karfi.

Ministan yada labaran ya ce, wannan ma somin tabi ne, domin kuwa gwamnati ta san cewa, kayan sun yi kadan, amma dai akwai wasu karin matakan tallafin gaggawa da za su biyo baya.

“Matsayin majalissar zartarwar ta kasa a nan shi ne kusan dai dukkan butatun masu zanga-zangar gwamnatin tarayyar ta ci karfinsu.”

“Shugaban kasa ya saurari muryoyin duka masu tsara wannan zanga-zanga, sakon kuma a nan shi ne babu bukata a gudanar da ita wannan zanga- zanga.” (Garba Abdullahi Bagwai)