logo

HAUSA

An yi tattaunawa kan jigon “zurfafa gyare-gyare a Sin dama ce ga duniya” a Najeriya

2024-07-30 16:18:17 CMG Hausa

Kwanan nan ne, sashin Hausa na babban rukunin gidajen rediyo da talabijin na kasar Sin wato CMG, da cibiyar tallata al’adun kasar Sin dake Najeriya, suka gudanar da taron tattaunawa mai taken “zurfafa gyare-gyare a kasar Sin a sabon zamani dama ce ga duniya” a birnin Abuja.

Mataimakin shugaban sashin fadakar da al’umma na kwamitin kolin jam’iyyar kwaminis ta kasar Sin, wanda kuma shi ne shugaban CMG Shen Haixiong, ya gabatar da jawabi ta kafar bidiyo. Wakiliya ta musamman daga ma’aikatar al’adun Najeriya, madam Narai Patricia, da shugaban kungiyar masu fasaha ta Najeriya, kana shugaban kungiyar daliban Najeriya da suka taba yin karatu a kasar Sin Mohammed Sulaiman, da sanannen dan jaridan Najeriya wanda ya kawo ziyara kasar Sin sau da dama Raphael Oni, da sauran wasu baki sama da 50, sun halarci taron, tare da gudanar da shawarwari game da babbar ma’anar zamanantarwa irin ta kasar Sin ga kasashen Afirka.

A jawabin nasa, Mista Shen Haixiong ya ce kasar Sin na ci gaba da zurfafa gyare-gyare a gida daga dukkan fannoni, tare da kokarin zamanantar da kasar. Ya ce, zurfafa gyare-gyare a cikin gida daga dukkanin fannoni, na kunshe da wasu muhimman manufofi, ciki har da tsayawa ga jagorancin jam’iyyar kwaminis ta kasar Sin, da mayar da muradun al’umma a gaban komai, da kara yin kirkire-kirkire, da tsayawa ga tafiyar da mulkin kasa bisa doka daga dukkan fannoni da sauransu, wadanda suka bayyana hikimomi gami da dabarun kasar Sin.

Mista Shen ya kara da cewa, zurfafa gyare-gyare a cikin gida daga dukkan fannoni a sabon zamanin da muke ciki da kasar Sin take yi a halin yanzu, wani muhimmin mataki ne da kasar ke aiwatarwa, wajen farfado da kasar gami da raya babban sha’anin gina kasa, al’amarin da babu shakka zai samar da sabon kuzari ga daukacin ‘yan Adam, don su lalubo hanyoyin zamanantar da kansu, da kyautata tsare-tsaren kasashensu.

Ya ce, a matsayin wata muhimmiyar kafar watsa labarai ta kasa da kasa a duniya, babban rukunin gidajen rediyo da talabijin na kasar Sin wato CMG, ya dade yana kokarin gabatar da rahotanni masu inganci, kan yadda kasar take himmatuwa wajen yin gyare-gyare a cikin gida da fadada bude kofa ga kasashen waje, da yadda kasar take kokarin zamanantar da kanta, da yadda take kokarin yin shawarwari da mu’amala tare da sauran kasashe. Mista Shen ya kara da cewa, muna fatan yin kokari tare da sassan kasa da kasa, don kara gina al’umma mai kyakkyawar makoma ta bai daya, da samar da makoma mai haske ga daukacin bil’adama.

Madam Narai Patricia, wakiliya ta musamman daga ma’aikatar kula da harkokin yawon bude ido ta Najeriya, ta bayyana a nata jawabin cewa, kokarin da ake na zamanantar da kasar Sin, ya samar da abubuwan koyi masu daraja ga Najeriya, musamman a fannonin da suka shafi raya sana’ar yawon bude ido, da kara samar da guraban ayyukan yi ga matasa, don rage hadarin dake tattare da mu’amalar mutane tsakanin birane da yankunan karkara.

Raphael Oni, sanannen dan jaridan Najeriya ne, wanda ya sha zuwa kasar Sin don gabatar da rahotanni ko ziyarce-ziyarce. A jawabin nasa, Oni ya ce, kasar Sin tana taka muhimmiyar rawa a fannin inganta kwarewar mutane a bangarori daban-daban dake Najeriya, kuma irin ci gaban da ta samu, ya samar da damammaki ga hadin-gwiwa da mu’amalar sassan kasa da kasa, al’amarin da ya zama kyakkyawan misali ga kasa da kasa ta fuskar inganta karfi da kwarewarsu.

Su kuwa shugaban kungiyar raya sana’ar yawon bude ido tsakanin matasan Najeriya OKON Emmanuel, da daliba wadda ta taba yin karatu a kasar Sin Edi-ima Friday, sun gabatar da jawabai ne na bayyana muhimmiyar rawar da matasa ke takawa a bangaren yawon bude ido, da kuma yadda kasar Sin ke maida hankali wajen samar da guraban karatu ga dalibai ‘yan kasashen waje, da bunkasa mu’amalar al’adu tsakanin Sin da sauran sassan duniya.

Daya daga cikin muhimman baki da suka halarci taron tattaunawar, malam Mohammed Sulaiman, wanda shi ne shugaban kungiyar masu fasaha ta baki dayan Najeriya, kana shugaban daliban Najeriya wadanda suka taba yin karatu a kasar Sin, shi ma ya bayyana nasa ra’ayi kan hadin-gwiwar kasar Sin da tarayyar Najeriya, da ma wasu muhimman fannoni da ya kamata kasashen biyu su fadada hadin-gwiwa da mu'amala tsakaninsu. (Murtala Zhang)