logo

HAUSA

Ministoci hudu na kusa da tsohon shugaban kasar Nijar Mohamed Bazoum sun amfana da sakin wucin gadi

2024-07-30 10:25:01 CMG Hausa

A jamhuriyar Nijar a ranar jiya 29 ga watan Julin da muke ciki, kotu ta ba da umurnin sakin talala ga wasu tsoffin ministocin guda hudu na gwamnatin tsohon shugaban kasa Mohamed Bazoum da sojoji suka sauke bayan juyin mulkin ranar 26 ga watan Julin shekarar 2023.

Daga birnin Yamai, abokin aikimu Mamane Ada ya aiko mana da wannan rahoto.

 

Su dai wadannan tsoffin ministoci guda hudu, sun kasance na hannun daman tsohon shugaban kasar Nijar Mohamed Bazoum na tsohuwar jam’iyyar gurguzu mai mulki ta PNDS-Tarayya. Wadannan kusoshin gwamnatin tsohon faraminista Ouhoumoudou Mahamadou, sun shiga hannun sojoji tare da kowane daga cikinsu a gidan kaso washe garin juyin mulkin sojoji na ranar 26 ga watan Julin shekarar 2023 a karkashin jagorancin shugaban kasa birgadiye Abdourahamane Tiani kuma shugaban kwamitin ceton kasa na CNSP. Kusan shekara guda ke nan, da wadannan tsoffin ministoci ake tsare da su a gidajen yari daban daban na kasar Nijar.

A ranar jiya Litinin 29 ga watan Julin shekarar 2024, aka samu labarin cewa wadannan ministoci sun amfana da sakin wucin gadi, a cewar lauyansu Maitre Illo Issoufou a lokacin da ’yan jarida suke tuntubar shi jim kadan bayan sakin mutanen nasa. Wadannan tsoffin ministoci guda hudu na tsofuwar gwamnatin faraminista Ouhoumoudou Mahamadou, sun hada da dokta Ahmat Djidoud tsohon ministan kudi, dokta Rabiou Abdou tsohon ministan fasali, Ibrahim Yacouba tsohon ministan makamashi da dokta Hama Souley, tsohon ministan cikin gida.

Mamane Ada, sashen hausa na CMG daga Yamai a jamhuriyyar Nijar.