logo

HAUSA

Darajar kayayyakin da aka yi jigilarsu ta kai Yuan tririliyan 167.4 a rabin farko na bana a kasar Sin

2024-07-30 10:43:38 CMG Hausa

Yau Talata, kungiyar hadin gwiwa ta jigilar kaya da sayo kayayyaki ta kasar Sin wato CFLP ta gabatar da bayanin tafiyar da harkokin jigilar kayayyaki na rabin farkon shekarar bana. Bayanin ya nuna cewa, cikin rabin farkon shekarar bana, an gudanar da harkokin tattalin arziki cikin yanayi mai karko, kana bukatun al’umma a fannin jigilar kayayyaki ya sami farfadowa kamar yadda ake fata.

Bayanin ya kuma kara da cewa, cikin rabin farkon shekarar bana, darajar kayayyakin da aka yi jigilarsu ta kai Yuan triliyan 167.4, adadin da ya karu da kaso 5.8 bisa dari idan aka kwatanta da na makamancin lokacin bara. A cikin kayayyakin kuma, jimillar jigilar kayayyakin da aka kera da fasahohin zamani ta karu da kaso 8.7 bisa dari, yayin da jimillar jigilar kayayyakin da aka shigo da su daga ketare ta karu da kaso 4.8 bisa dari, bisa na makamancin lokacin bara.

A fannin yin sayayya kuma, jimillar jigilar kayayyakin da kamfanoni da al’ummun kasar Sin suka saya ta karu da kaso 8.7 bisa dari, idan aka kwatanta da na makamancin lokacin bara. Kaza lika, yawan kudaden da aka kashe domin sayan kayayyaki ta yanar gizo, ya karu da kaso 8.8 bisa dari, adadin da ya kai kaso 25.3 bisa dari na jimillar kayayyakin da aka sayarwa cikin kasar. (Mai Fassara: Maryam Yang)