logo

HAUSA

An rattaba hannu kan yarjejeniyar hadin gwiwa tsakanin CMG da AL

2024-07-30 20:50:22 CMG Hausa

A yau Talata ne babban sakataren kungiyar tarayyar kasashen Larabawa ta AL Ahmed Aboul Gheit, ya gana da mataimakin shugaban sashen yada bayanai na kwamitin kolin JKS, kuma shugaban babban rukunin gidajen radio da talabijin na kasar Sin CMG mista Shen Haixiong, a birnin Alkahiran kasar Masar. Yayin tattaunawar, manyan jami’an biyu sun yi musayar ra’ayoyi game da batutuwan da suka shafi raya al’adu, da wasanni, da hadin gwiwar watsa shirye shirye da sauransu. Kaza lika, sassan biyu sun rattaba hannu kan yarjejeniyar hadin gwiwa.

Har ila yau a dai jiyan, Ahmed Aboul Gheit ya gabatar da takardar shaida ta "wakilin sada zumunta tsakanin Sin da kasashen Larabawa " ga CMG, don yaba kwazon sa a fannin ingiza abota tsakanin Sin da kasashen Larabawa.  (Saminu Alhassan)