logo

HAUSA

Cinikayyar Sin da kasashen ketare ta kafar intanet ta samu bunkasuwa mai kyau

2024-07-30 14:31:39 CMG Hausa

Rahoton kwastam na kasar Sin ya nuna cewa, a watanni shida na farkon wannan shekara ta 2024, yawan cinikayyar kasar Sin da kasashen ketare ta kafar intanet ya kai yuan triliyan 1.22 kwatankwacin dalar Amurka biliyan 170.95, wanda ya karu da kashi 10.5 cikin dari bisa na shekarar da ta gabata.

Kakakin hukumar kwastam Lyu Daliang ya shaidawa taron manema labarai cewa, an samu bunkasuwa ne ta hanyar manufofin tallafi da suka hada da kafa yankunan gwaji don bunkasa kasuwanci da kasashen ketare ta kafar intanet da kuma saukaka ayyukan kwastam.

Bugu da kari, jimillar yawan cinikin kasar Sin ya kasance a matsayi na daya a duniya tsawon shekaru bakwai a jere, kuma ta zama babbar abokiyar cinikayya tsakanin kasashe da yankuna fiye da 150. (Mohammed Yahaya)