Za a gudanar da taron kolin dandalin FOCAC na shekarar 2024 tun daga ranar 4 zuwa 6 ga watan Satumba a birnin Beijing
2024-07-30 10:50:09 CMG Hausa
Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Hua Chunying ta sanar a yau cewa, za a gudanar da taron koli na dandalin tattaunawa kan hadin gwiwar Sin da Afirka wato FOCAC na shekarar 2024 tun daga ranar 4 zuwa 6 ga watan Satumba a birnin Beijing, fadar mulkin kasar Sin. Kana taken taron a wannan karo shi ne “Hada kai a kokarin tabbatar da zamanintarwa da neman raya al’umma mai kyakkyawar makomar bai daya ta Sin da Afirka mai inganci”. A cewaer kakakin, shugabannin kasashen Afirka membobin dandalin FOCAC za su halarci taron bisa gayyatar da aka yi musu, kana wakilan kungiyoyin Afirka da na kasa da kasa da abin ya shafa su ma za su halarci taron. (Zainab Zhang)