logo

HAUSA

Kasar Sin na maraba da karin abokan tafiya don shiga hadin gwiwar BRICS

2024-07-29 20:33:59 CMG Hausa

Mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Lin Jian, ya ce kasarsa tana maraba da abokan huldar da ke da ra’ayi iri daya, da su shiga cikin hadin gwiwar kasashen BRICS, tare da sa kaimi ga bunkasa tsarin kasa da kasa bisa hanyar da ta dace.

Jami’in ya bayyana hakan ne a yayin da yake ba da amsa kan bukatar kasar Malaysia na shiga cikin tsarin hadin gwiwa na BRICS, a gun taron manema labaru da aka saba yi a yau Litinin 29 ga watan nan, inda ya kara da cewa, ci gaban tsarin BRICS ya dace da yanayin zamani, wanda kuma ya dace da muradun kasashe daban daban, kuma yana ba da kwarin gwiwa ga raya harkokin duniya mai bangarori da dama, da dimokuradiyyar dangantakar kasa da kasa.

Kaza lika dangane da furucin da ministocin harkokin wajen Amurka, Japan, da sauran kasashe suka yi, game da damuwarsu kan halin da ake ciki a tekun gabashin kasar Sin, da tekun kudancin kasar, jami’in ya bayyana cewa, kasar Sin ta bukaci kasashen dake wajen yankin, su mutunta hakikanin kokarin da kasashen yankin suke yi, na wanzar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a yankin, tare da kaucewa hura wutar rikici ga yanayin yankin. (Bilkisu Xin)