logo

HAUSA

Shugaba Xi ya gana da firaministar Italiya

2024-07-29 21:14:23 CMG Hausa

A yau Litinin shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya gana da firaministar kasar Italiya Giorgia Meloni a birnin Beijing. Yayin zantawar su shugaba Xi, ya ce kasar sa da Italiya na kan iyakokin karshe na tsohuwar hanyar siliki, kuma kawancen musamman na tsawon lokaci tsakanin kasashen biyu ya samar da babbar gudummawa ga daukacin musaya, da koyi da juna tsakanin wayewar kan gabashi da yammacin duniya, tare da tallafawa ci gaban bil adama.

Shugaban na Sin ya kara da cewa, ruhin hanyar siliki na zaman lafiya da hadin gwiwa, da yin komai a bude, da tafiya tare da dukkanin sassa, da koyi da juna, da cimma moriyar juna, sun kasance wata haja mai kima da Sin da Italiya suka raba tsakanin su.

Daga nan shugaba Xi ya ce kamata ya yi sassan biyu su goyi baya, da yayata ruhin hanyar siliki, su nazarci tare da bunkasa alakar dake tsakanin su ta mahangar tarihi, da burin cimma nasara ta tsawon lokaci, tare da ingiza alakar su bisa daidaito.   (Saminu Alhassan)