Kasar Sin ta samu ci gaba a rigakafin cutar hanta
2024-07-29 10:48:13 CMG Hausa
Yayin da aka yi bikin ranar yaki da cutar hanta ta duniya na bana a ranar Lahadi, jami’ai da kwararru na kasar Sin sun bayyana gagarumin ci gaba da kasar ta samu wajen rigakafin cutar hepatitis, wato kumburin hanta da ke haifar da matsanancin cutar hanta da kansa.
Mataimakin shugaban hukumar kula da rigakafin cuttutuka ta kasar Chang Jile ya ce, cuttutuka da suka shafi cutar hanta sun ragu a kasar, sakamakon kara sanya ido da kuma daukar matakan da suka dace.
Bayanai sun nuna cewa yawan kamuwa da cutar hanta ta Hepatitis B na ci gaba da raguwa a kasar musamman a tsakanin yara ’yan kasa da shekaru 5, inda aka iyakance ta zuwa kasa da kashi 1 cikin dari. Hepatitis B na daya daga cikin cututtukan da ke yaduwa a duniya kuma an dauke ta a matsayin muhimmin batun lafiyar jama'a a kasar Sin. (Mohammed Yahaya)