logo

HAUSA

Firaministan Lebanon ya yi kira da tsagaita wuta a Kudancin Lebanon

2024-07-29 10:40:50 CMG Hausa

Firaministan kasar Lebanon Najib Mikati a jiya Lahadi ya yi kira da a tsagaita bude wuta a kudancin kasar Lebanon tare da aiwatar da kudurin Majalisar Dinkin Duniya mai lamba 1701 don kaucewa tabarbarewar tsaro.

A cikin wata sanarwar da ofishin Mikati ya fitar, ya jaddada matsayin gwamnatin kasar na yin Allah wadai da duk wani nau’i na cin zarafi da ake yiwa fararen hula, kuma tsagaita bude wuta ta kowane bangare ita ce hanya daya tilo da za ta magance tashe-tashen hankula da kuma kaucewa tabarbarewar al’amura a kasar.

Sanarwar ta kara da cewa, firaministan ya gudanar da jerin tuntubar diflomasiyya da siyasa don bin diddigin lamarin gaggawa da kuma barazanar da Isra'ila ke ci gaba da yi wa kasar Lebanon.

Yanayin da damuwa da tashin hankali ya mamaye yankin kan iyakar kudancin kasar Lebanon bisa la'akari da barazanar da Isra'ila ta yi na kaddamar da farmakin soji da zai sanya kungiyar Hizbullah "ta yi da ta sani" kwana guda bayan harin wani makami mai linzami a garin Majdal Shams dake Tuddan Golan da Isra'ila ta mamaye, inda ya kashe mutane 12 tare da jikkata wasu da dama. (Mohammed Yahaya)