logo

HAUSA

Kungiyar daliban Najeriya ta tsame kanta daga shirye-shiryen zanga-zangar gama gari da ake yi a kasar

2024-07-29 09:25:36 CMG Hausa

Shugabancin kungiyar daliban Najeriya ta ce, ba za ta shiga cikin shirin zanga-zangar da ake kokarin gudanarwa a kasar cikin watan gobe ba.

Shugaban kungiyar na kasa Mr. Lucky Emonefe ne ya tabbatar da hakan a karshen makon jiya lokacin da ya jagoranci manyan shugabannin kungiyar zuwa ofishin ministan ilimin kasar, a saboda haka nema shugaban ke umartar dukkannin daliban dake jihohin kasar, ciki har da Abuja da su janye jikinsu daga shiga cikin jerin gwanon masu zanga-zangar.

Daga Tarayyar Najeriya wakilinmu Garba Abdullahi Bagwai ya aiko mana da rahoto. 

Shugaban kungiyar daliban ta Najeriya Mr Lucky Emonefe ya ce, daliban Najeriya da suke sa ran zaman manyan gobe, ba za su taba amincewa ba a yi amfani da su wajen lalata makomar kasa ta hanyar haifar da rikici da zai iya shafar zaman lafiyar Najeriya.

Shugaban ya tabbatarwa ministan ilimin cewa ko kadan babu wani dalibi da zai kasance cikin zanga-zangar, inda ya kara shaidawa ministan cewa sun yanke shawarar kin shiga zanga-zangar ne saboda irin sauye-sauye masu ma’ana da shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya bullo da su musamman ma a bangaren ilimi inda a kwanan nan ne ya amince da ba da rancen karatu ga dalibai abun da ba’a taba yi ba a kasa.

Shugaban kungiyar daliban ya ce, hakika ’yan Najeriya na fama da yunwa da tsadar rayuwa wanda wannan bai kyale dalibai ba, amma duk da hakan kungiyar daliban ta ga dacewar a kara yiwa gwamnati uzuri domin ta sami nasarar gyare-gyaren da take yi a tattalin arzikin kasa.

“Muna son mu yi amfnai da wanann dama a matsayin mu na dalibai da muka yanke shawarar kasancewa masu bin doka ta wajen  kin bin ra’ayin masu son tayar da hargitsi a cikin al’ummarmu. Muna kira ga minista da ya bukaci shugaba Tinubu ya kara mayar da hankalinsa kan yanayin rayuwar dalibai.” (Garba Abdullahi Bagwai)